Revelation of John 6

1Na duba lokacin da Dan Ragon ya bude daya daga cikin hatiman bakwai, sai na ji daya daga cikin rayayyun halittattun hudu ya fada da murya kamar tsawa, ‘’Zo!” 2Sai Na duba sai ga wani farin doki, mahayinsa na rike da baka, kuma an bashi rawani. Ya fito a matsayin mai nasara domin ya yi nasara.

3Sa’anda Dan Ragon ya bude hatimi na biyu, sai na ji rayayyen halitta na biyu ya ce, ‘‘Zo!‘’ 4Sai wani doki ya fito waje - jawur. Ga mahayin aka bashi dama ya dauke salama daga duniya, domin mutanen ta su karkashe juna. Wannan mahayin an bashi babbar takobi.

5Sa’anda Dan Ragon ya bude hatimi na uku, sai na ji rayayyen halita na uku ya ce, ‘‘Zo!‘’ Na ga bakin doki, mai hawanta na rike da ma’auni a cikin hannunsa. 6Sai na ji kamar wata murya daga cikin rayayyun halittattun nan hudu ta ce, “Mudun alkama guda a kan albashin yini, kuma mudun sha’ir uku. Amma kar ka bata mai da kuma ruwan inabi.”

7Da Dan Ragon ya bude hatimi na hudu, na ji muryar rayayyen halitta na hudu ya ce, ‘‘Zo!‘’ 8Sai na ga wani doki ruwan toka. Mai hawansa an bashi suna mutuwa, hades kuma tana biye da shi. An basu iko bisa kashi hudu na duniya su kashe da takobi, yunwa, cututtuka, da kuma namomin jeji na duniya.

9Da Dan Ragon ya bude hatimi na biyar, a karkashin bagadi sai na ga rayukan wadanda aka kashe saboda maganar Allah, da kuma shaidar da suka rike. 10Suka yi kuka da babban murya, ‘’Sai yaushe ya mai iko duka, Mai Tsarki da gaskiya, zaka shari’anta mazaunan duniya, ka kuma dauki fansar jininmu? 11Sai kowanne dayan su aka bashi farar tufa aka kuma fada masu su kara jira na lokaci kadan har sai adadin abokan bautar su da kuma ‘yan’uwansu maza da mata wadanda aka kashe ya cika, kamar yadda aka kashe su.

12Da Dan Ragon ya bude hatimi na shidan, ina kallo sai ga babbar girgizar kasa. Rana ta zama baki kirin kamar bakar tufa, wata kuma ya zama kamar jini. 13Taurarin sama suka fado kasa, kamar yadda itacen baure ke karkade ‘ya’yansa da basu nuna ba, yayin da babbar iska ta kada. 14Sama kuma ta bace kamar takardar da aka nannade. Kowanne dutse da tsibiri aka kau da shi daga wurinsa.

15Sai sarakan duniya da muhimman mutane da sarakunan yaki, attajirai, da masu iko, tare da kowanne mutum, bawa da ‘yantacce suka boye cikin duwatsu da tsaunuka. 16Suka ce wa tsaunuka da duwatsu, “Ku fado bisan mu! Ku boye mu daga fuskar wanda yake zaune bisa kursiyin da kuma fushin Dan Ragon. Domin babban ranar fushin sa ta zo. Wa zai iya tsayawa?‘’

17

Copyright information for HauULB